A’uzu billahi minash Shaidanir Rajeem.Bismillahir Rahmanir Raheem.Wasallallahu ala Muhammadin wa Alihid Dayyibinad Dahireen.Allahumma Salli ala Muhammad wa Ali Muhammad.
“Bismillahir Rahmanir Raheem.Qul inna Salatiy wa nusukiy wa mahyaya wa mamatiy lillah”
Ma’ana; “Kace(Ya Manzon Allah): Hakika sallata da nusuk dina da rayuwata da mutuwata duka don Allah ne”.
Wannan shine “kulasa”na shaksiyyar Manzon Allah(sawa) kaman yanda Allah Subhanahu wa Ta’ala ya so mu fahimta dangane da shaksiyyar Manzon Allah (sawa) din.
Rayuwar Manzon Allah (sawa),ba rayuwar shi ba,komai da komai nashi Manzon Allah na Allah ne kuma domin Allah Subhanahu wa Ta’ala ne.Saboda “maraatib” na “Al-qubul Ilahiy”wanda Manzon Allah(sawa) ya zama cewa ya tsallake,wanda a wurare da yawa mun yi bayanin wa’yannan akan asasin abinda malamai suka bayyana a mahallai da suka bayyanar.
Dukkan shaksiyya ta Manzon Allah(sawa),shaksiyya ce “Ilahiyyah”.Wannan ya hada da ibadun Manzon Allah(sawa) wa’yanda suke sune “sila” da Allah Subhanahu wa Ta’ala din “mubasharatan”, da sharudda da kaifiyyoyi na wa’yannan ibadun,da zamantakewa ta Manzon Allah(sawa) a cikin iyalinshi,da a cikin Sahabbanshi,da a cikin mutane gabaki daya,da kuma dangantakarshi da “kaun”,da rayuwarshi ta zamantakewa “Al-ijtima’iy”.
Babu wani tasarruf a cikin shaksiyya din Manzon Allah (sawa) wanda yake ba tasarrufi bane “ilahiy”,babu.Shi yasa in yayi magana Manzon Allah(sawa) maganar ta kan zama wahayi.Yaya a yau in aka zabi mutum ya zama gwamna ko ya zama shugaban kasa sai ya zama lufuzzan da yake yin “nuduqi” magana dasu dukkansu suke zama “awaamir” ko ya rubuta ko bai rubuta ba-ban san ko an gane abinda nake nufi ba.Idan gwamna yana magana ko idan shugaban kasa yana magana a tsarin da muke ciki a yau,dukkan abubuwan da yake fadi “official” ne wato “rasmiyyai” ne.
Ko da wasa yayi umurni da wani abu ya zartu ko?Fiye da haka Manzon Allah(sawa) yake,da ma’anar cewa “nuduqin” shi Manzon Allah (sawa) dabbaqaqqe ne akan “nafsul amr”, akan waqi’a,akan ilimin Allah Subhanahu wa Ta’ala,akan matakin wahayi.Shi yasa ba bambamci tsakanin abinda Manzon Allah(sawa) ya fadi da kashin kanshi da kuma abinda Allah Subhanahu wa Ta’ala ya fadi ta hanyar Manzon Allah(sawa) a Al-Kur’ani,a mustawa ta karfin “hujjiyyah”-wannan bahsi ne muqarrar a muhallinshi.
Shi yasa suka ce wahayi kala biyu ne,wani wahayi sunanshi Al-Kur’ani,wani wahayin kuma sunanshi Hadith.Bambamci tsakanin su biyun shine tarkibin jumlolin da sakon da ma’anar duka daga Allah Subhanahu wa Ta’ala ne a Al-kur’ani amma sakon da ma’anar daga Allah Subhanahu wa Ta’ala ne amma tarkibin jumlolin daga Manzon Allah (sawa) a Hadith.
In kace to menene matsayin Al-Hadithul Qudsi,sai a ce maka shima Al-Hadithul Qudsi a tarkibin jumlolin sabaninshi da Al-Hadith Annabawiy.Tarkibin jumlolin da ma’ana da sakon duka daga Allah (T) ne da bambamcin cewa a Al-Kur’ani akwai “ta’ajiz” amma a Al-Hadith Al-Qudsi babu “ta’ajiz”,shine kawai bambamci.
Ala kullil ahwal,nuduqin Manzon Allah (sawa) wahayi ne.Ayyaukan Manzon Allah(sawa) wahayi ne,lafuzzan Manzon Allah (sawa) wahayi ne,hukunce hukuncen Manzon Allah gabaki dayansu wahayi ne.Dukkanshi gabaki dayanshi domin Allah,shi yasa ya cancanta ya zama “uswa” wato ya zama samfuri abin koyi .
Allah Subhanahu wa Ta’ala Yana cewa a cikin Al-Kur’ani a Suratul Ahzab:
“LAQAD KANA LAKUM FI RASULILLAHI USWATUN HASANATUN LIMAN KANA YARJUL LAHA WAL YAUMAL AKHIRA,WA ZAKARALLAHA KASIRAN
Ma’ana: Hakika “uswa” ta kasance maku a cikin Manzon Allah (sawa) ga wanda ya kasance yana kwadayin Allah,yana fatan haduwa da Allah da ranar karshe,kuma ya ambaci Allah da yawa(ya zama kullum yana cikin hudur ne,wato baya cikin gafla).
Wanda yake da wa’yannan siffofin uku,to Manzon Allah (sawa) uswa ne gare shi.Allamah Tabataba’I yana cewa “uswa” da ma’anar “qudwa” da ma’anar “namuzaj” wato shugaba,jagora,samfuri wanda aka ajiye shi a gabanka domin ka kwaikwaye shi a komi da komi naka,ka zama hikaya na Manzon Allah (sawa).Wanda yayi haka shi ya rabauta,wanda ya kauce daga barin haka bayan shiriya ta riga ta bayyana mashi,za a jibanta mashi abinda ya jibanta ma kanshi,wato tasarrofofinshi nashi ne,kenan ba na Allah (t) ba.Zai zama yana tafiya akan asasin iyakoki wa’yanda yake babu yakini.
Wannan gabaki dayanshi a matsayin shimfida saboda munasabar wannan watan na ma’abucin munasaban,wato kenan watan Rabi’ul Auwal wanda a cikinshi ne akan haifi shi Manzon Allah(sawa).
Muna so mu kawo wasu darussa daga rayuwan Manzon Allah(sawa) wanda muke fatan dabbaqa su a aikace a cikin rayuwanmu a wannan duniyar.
An fadi abubuwa masu yawan gaske dangane da shaksiyya ta Manzon Allah (sawa) da darussa da yake za a amfana dasu a cikin wannan shaksiyya din RABBANIYYAH,ILAHIYYAH wadda muka ce ta tsallake dukkan “maraatib” na “Al-Qurbul Ilahiy” wanda wani “mumkin” bai iya kaiwa gare su ko tsallake.
An ambaci abubuwa masu yawa kaman yanda muka ce.A nan zamu fadi wasu,sannan sai muyi amfani da wannan daman mu ce wani abu dangane da Al-Imam Husain(as),sannan mu hada darasin Al-Imam Husain da darasin shaksiyya din Manzon Allah(sawa) din saboda Al-Imam Al-Husain (as) dukkan rayuwanshi hikaya ce ta Manzon Allah(sawa) “tamaman”.Sai mu ga cewa ya bambamta da Manzon Allah ko bai bambamta ba?.288
26 Disamba 2016 - 20:01
News ID: 800982
Na Maulana Al-Mujahid Sheikh Hamzah Muhammad Lawal Yusuf Sulaiman ya rubuta maku.